Wannan umarnin tsagaita wuta, Ministan Tsaro na Rasha Sergei Shoigu ya sanar inda yake cewa daga gobe Talata za’a sami sassauci na tsagaita wuta tsakanin karfe tara zuwa biyu na rana, saboda a samu a kai tallafi ga mabukata.
Tun da fari a yau littini shugaban Faransa Emmanuel Macron da takwaransa na Turkiya Recep Tayyip Erdogan sun tattauna batun Syria ta wayan talho inda suka nemi a tsagaita wuta a yakin na Syria kuma lallai a hada da yankin Afrin inda Turkiya ke ta barin wuta kan kurdawa
Shugaban Faransa ya fadi cewa tsagaita wutan na tsawon kwanaki 30 ya hada da dukkan sassan Syria wato har da yankin Afrin.
A yau din nema Gwamnatin Turkiya ke fadin cewa ta tura karin Dakaru domin yakin sosai a yankin na Syria.